Jum'a 17 ga Rabi'ussani, 1440 | Bugu na 1380 | ISSN 1595-4474 |
---|
Gobe Zaben Shugaban Kasa: Wa Zai Sha Kaye?
Gobe Asabar 16 ga Fabrairu, 2019 ne ake sa ran bude rumfunan zaben Shugaban kasa, wanda Hukumar zabe mai zaman kanta za ta gudanar a duk fadin kasar nan. Sai dai tambayar da masana da kuma masu nazarin harkokin siyasar kasar suke yi ita ce, shin wa zai sha kaye a gobe?ci gaba
Harkar Musulunci a Nijeriya ta samu wasu sahihan rahotannin da suka nuna cewa, an ga wasu mutane da ba a san su ba dauke da muggan makamai a ranar Alhamis, 07/02/2019 a wasu sassan Zariya, jihar Kaduna, musamman a yankin Sabon gari.ci gaba
Miliyoyin Iraniyawa sun fito gangamin cika shekaru 40 Da nasarar Juyin-Juya-Halin Musulunci a kasar
An bayyana cewa take hakkin Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa shi ne mafi munin take hakkin Bil’adama a tarihin kasar nan tun bayan mulkin-mallaka na Turawa.ci gaba
Rahotannimu
Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi hira a gidajen rediyon Kano inda ya tattauna a kan manyan batutuwan da suka shafi zaben 2019 da yake kusantowa a Najeriya.
‘Har yanzu ana kashe mutane a yankin Birnin Gwari’ in Sanata Shehu Sani
Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana wa manema labarai cewa, har yanzu ana ci gaba da kashe mutane a yankin Birnin Gwari.
Hako mai a Bauchi: Masu filin sun ce ba a biya su kudin diyya ba
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya kamata ya hakura da neman ta-zarce a shekarar 2019, saboda yawan shekaru da yanayin lafiyarsa, don haka ya tafi gida kawai ya huta.
Cutarwar 'yan Izala ga 'yan Shi’a a Najeriya (xiii)
Kasar nan ba ta ga canji na alheri ba -Sanata Mamman Abubakar Dan Musa
Jawabai da Karatun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H):
Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.
Labaran Harka Islamiyyah
Babban abin al’ajabi a waki’ar Zariya - Cewar Sayyid Badamasi Yakub Zakzaky Ra'ayin Almizan TAKARDAR MANEMA LABARAI
Kwanaki 700 na haramtacciyar tsarewa: Kiranmu na kin ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky a sarari yake, kudurinmu kuma bai girgizu ba!
Daga Gidan Annabta Tare da Abubakar Abdullahi Almizan
KU KYAUTATA WA MAMATAN KU (1)
An ruwaito Hadisi daga wasu cikin Sahabban Annabi (S) suka ce; Manzon Allah (S) yana cewa: “Ku bayar da kyauta ga mamatanku”. Sai muka ce; Ya Manzon Allah (S) ta yaya ne za mu yi kyauta ga mamatanmu?
Katun
Tunatarwa:
Tare da Sheikh Zakzaky
P>Saboda haka wannan rana ce da ta nuna sasantawa tsakanin musulmi da Kirista. Har ma akwai ayar da take cewa, za ka ga wadanda suka fi kusa da son muminai, wato in na ce musulmi za a fi ganewa, sune wadanda suka ce mu Kirista ne. Allah (T) ya ce, saboda a cikin su akwai Malamai akwai masu ilimi, ku su ba su da girman kai. Wannan yabo ne ga Kiristoci, cewa cikin su akwai masu ilimi, kuma ba su da girman kai. Shi ya sa suka fi kusa da son musulmi.
Tambihi:
Tare da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna
“Wamakaru wamakarallah, wallahu khairul makirin. Kasantuwar wannan hali da kuma yanayi da muke ciki na jarabawa, jarabawa wadda a tarihin wannan Harka ba a taba fuskantar irinta ba, misali mutum ya kwatanta adadin shahidan da aka samu a wannan waki’a da kuma adadin shahidan da aka samu a tsawon tarihin wannan, Harka zai ga cewa sun nunnuka su.